<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Yau Ranar Murna Ce LW563</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yau ranar murna ce ga mu masu bin Yesu
 Domin jinkansa, da alherinsa
 Sai ku zo mu yi tsale, mu ɗaukaka Allah Uba
 Domin ƙaunarsa, a garemu
 Domin cetonsa, ta wurin Yesu ɗan Allah
 Solo: &quot;Sai ku zo.&quot;

[V2]
 KORUS
 Sai ku zo mu yi murna
 Mu ɗaukaka Allah Uba
 Mu miƙa godiyarmu
 Ga Allah mai kamnar duniya
 Solo: &quot;Sai ku zo.&quot;

[V3]
 2) An haifi Yesu a Baitalahmi
 Daga budurwa, Maryamu
 Aka haife shi, a cikin garke
 Aka naɗe shi..., cikin tsummoki
 Shi ke ɗan Allah, mahalicin Sama da kasa
 Solo: &quot;Sai ku zo.&quot;

[V4]
 3) Ruhun Yahweh, yana a kansa
 Ya rufe shi da rigar adalci
 Ya aiko shi..., don ya kawo yanci
 Ga waɗanda, ke cikin zunubi
 Don Ya bamu rai, na har abada abadin
 Solo: &quot;Sai ku zo.&quot;</lyrics>
<hymn_number>563</hymn_number>
</song>